Me ya sa 'yandaba ke kai wa Isra'ilawa hari a Sweden? - BBC News Hausa (2025)

Me ya sa 'yandaba ke kai wa Isra'ilawa hari a Sweden? - BBC News Hausa (1)

Asalin hoton, Alex Maxia/BBC

Bayani kan maƙala
  • Marubuci, Alex Maxia
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, In Gothenburg
  • Aiko rahoto daga Sweden

Ya kamata a ce yaron mai shekara 13 yana makaranta ranar Alhamis ɗin da ta gabata a maimakon kasancewa a ofishin ƴansanda a Gothenburg.

Sai dai ƴansanda sun ce sun yi harbe-harbe a wajen kamfanin fasahar Isra'ila - Elbit Systems.

"An same shi dumu-dumu da laifin," in ji Kakakin ƴansanda August Brandt wanda ya ce ana yin bincike kan harbe-harben kuma ana tunanin "yunƙuri ne na kisa da kuma laifin mallakar makamai".

Kalleback da ke wajen Gothenburg, wata unguwa ce mara hayaniya da ke da shagon sayar da kayayyaki da kuma ofisoshi kaɗan.

Babu wanda ya ji rauni sannan babu ƙarin bayani kan abin da ya sa yaro ya buɗe wuta a irin wurin da babu hayaniyar jama'a da safiyar Alhamis, a wajen kamfanin Isra'ila mai sayar da kayan tsaro.

Sai dai ba wannan ne karon farko ba, an taɓa samun faruwar irin haka lokuta da dama a wannan shekarar.

Tun a farkon watan nan ne ake harar ofisoshin jakadancin Isra'ila a Sweden da Denmark.

Farko, an yi harbe-harbe a wajen ofishin jakadancin Isra'ila a Stockholm, sai kuma aka kama wasu matasa ƴan shekara 16 da 19 a Copenhagen bayan fashewar gurneti kusa da ofishin jakadanci a can.

Babu wanda ya jikkata sai dai jami'an tsaron Sweden, Sapo sun ce wataƙila Iran na da hannu a harin biyu.

Shugaban sashen kula da al'amura na Sapo Fredrik Hallstrom ya ce sa hannun Iran ɗin abu ne da ake iya hasashe.

Me ya sa 'yandaba ke kai wa Isra'ilawa hari a Sweden? - BBC News Hausa (3)

Asalin hoton, Reuters

Watanni da suka gabata, Sapo ta zargi Iran da ɗaukar wani gungun ƴandabar Sweden aiki domin su kai hare-hare kan Isra'ila ko wuraren Yahudawa.

Ma'aikatar harkokin wajen Iran sun yi allawadai da zarge-zargen inda suka ce ba su da tushe bare makama da ke samun asali daga jita-jitar da Isra'ila ke yaɗawa.

Galibin waɗanda ake zargi matasa ne wasu ba su wuce shekara 13 da 14 ba.

"Domin fahimtar abin da ya sa matasan Sweden ke kai hare-hare kan kamfanonin Isra'ila da ofisoshin jakadancinta, akwai buƙatar mu fahimci cewa akwai rikicin ƴandaba da ake yi a nan Sweden tsawon lokaci," in ji Diamant Salihu, wani ɗan jarida mai binciken ƙwaƙwaf da ke aiki a gidan talabijin na ƙasar Sweden SVT.

Ɗaya daga cikin ƙungiyoyi masu aikata miyagun laifuka a Sweden da ake kira Foxtrot, sun kawo wani sabon tashin hankali a titunan Sweden, galibin ake tura ƙananan yara aikata miyagun laifuka kama daga harbe-harbe zuwa fasa abin fashewa.

Lamarin ya yi ƙamari a 2023 lokacin da shugaban gungun Foxtrot Rawa Majid ya shiga wani mummunan rikici da Isma'il Abdo, tsohon abokinsa da ya zama jagoran wata ƙungiyar daba mai suna Rumba.

Lokacin da aka kashe mahaifiyar Abdo a gidanta da ke Uppsala, a arewacin Stocholm a Satumbar bara, hakan ya ƙara janyo ƙaruwar tashin hankali tsakanin gungun ƴandabar Sweden.

A lokacin, an gano wasu ƴan shekara 15 da 19 ne suke da hannu a kisan.

Majid ya tsere zuwa ƙasashen waje inda yake fuskantar barazanar kamawa daga ƴansandan duniya, Interpol da kuma jerin maƙiya da ke ƙaruwa.

Haifaffen Iran, Abdo ya koma Sweden tun yana yaro tare da iyalinsa.

Ya bar Sweden zuwa Turkiyya a 2018 daga nan kuma ya yada zango a Iran a bara.

Hukumar leƙen asirin Isra'ila Mossad ta yi zargi cewa Majidya shafe watanni yana aiki tare da Iran. Ta zargi Abdo da gungun ƴan dabarsa da hannu a hare-haren baya-bayan nan.

Lokacin da shugaban sashen tattara bayanan sirri, Daniel Stenling ya ce Sapo "na iya tabbatar cewa ƙungiyar masu aikata miyagun laifuka a Sweden mutane ne da Iran ke amfani da su," Iran ta yi sammacin babban jami'in diflomasiyyar Sweden a Tehran domin nuna adawa.

Ita ma Sweden ta nemi a cafke abokin gwabzawar Majid, Isma'il Abdo, wanda aka kama a Turkiyya a watan Mayun bara amma aka sake shi bayan ba da belinsa.

Ɗanjarida Diamant Salihu ya ce Tehran ta nemi ta shawo kan gungun don aikata laifuka ga gwamnatin,” ko da yake 'yan dabar Abdo sun musanta hannun Iran a lamarin.

Yayin da ƙasashen yamma suka matsa wa ƙungiyar dabar lamba, matasan sun nuna ko a jikinsu waɗanda suka yi kaurin suna wajen aikata ayyukan daba a kasar.

An yi ƙiyasin cafke mutum 14,000 a Sweden da ake zargi da ayyukan daba, kuma 'yan sanda sun ce wannan a shekarar nan ne kaɗai, an kuma kama wasu 48,000 da ake zargi da taimaka mu su aikata muggan laifukan.

Me ya sa 'yandaba ke kai wa Isra'ilawa hari a Sweden? - BBC News Hausa (4)

Asalin hoton, ANDERS WIKLUND/TT NEWS AGENCY/AFP

“Yara matasa 'yan shekara 13 zuwa 14 da a yanzu aka kama da aikata muggan laifukan, su ne 'yan yaran nan shekaru 10 da suka gabata,'' in ji Firai Minista Ulf Kristersson lokacin da akai muhawarar shugabnnin jam'iyyun siysa da aka yada kai tsaye a gidan talbijin a karshen mako.

Muhawarar dai ta karkare da za ma ta nuna yatsa da dora laifi kan 'yan siyasa da jam'iyya mai mulki.

Tsohon firai ministan kasar na jam'iyyar Social Democrat, Magdalena Andersson ya yi kiran “a dauki sabon salon yaki da matsalar” amma Kristerssonya ce inda za a samu babbar matsalar shi ne yadda ake matsalar ta fi fitowa daga 'yan cirani.

David Sausdal, kwararren mai bincike kan aikata muggan laifuka a jami'ar Lund da ke kudancin Sweden ya ce a yanzu lamarin na da wuya a sanya ido da bibiyar yadda kungiyoyin daba ke gudanar da ayyukansu musamman ta intanet, inda suke amfani da shafukan intanet wajen jan hankalin mutane da amfani da halin matsin tattalin arziki da ake fama da shi a duniya.

"Ana hayar mutanen da suke aikata laifukan, a biya su kudi su gabatar da aiki. Ana aikensu kai sakon gurneti ko bindiga tamkar yadda za su kai sakon pizza.

“Ba su da kaifin basira, ba wani kwarin gwiwa da ake ba su ko a kambama aikin da su ke yi,kawai ma'aikata ne da ke kai sako.”

'Yan sanda da 'yan siyaras Sweden sun damu matuka, kan rin wannan sauyin da aka samu cikin al'umar kasar.

Ministan shari'a Gunnar Strommer, ya bayyana abubuwa uku da ke barazana ga tsaron kasar, da suka hada da ta'addanci, masu aikatawa na cikin gida da kungiyoyin da ke kitsa su.

Sai dai David Sausdal, ya ce harin dabar da aka kai a baya-bayan nan, ya wuce tunani da fahimta idan aka kwatanta da wadanda aka aikata a baya.

Me ya sa 'yandaba ke kai wa Isra'ilawa hari a Sweden? - BBC News Hausa (2025)
Top Articles
Latest Posts
Recommended Articles
Article information

Author: Clemencia Bogisich Ret

Last Updated:

Views: 5465

Rating: 5 / 5 (80 voted)

Reviews: 87% of readers found this page helpful

Author information

Name: Clemencia Bogisich Ret

Birthday: 2001-07-17

Address: Suite 794 53887 Geri Spring, West Cristentown, KY 54855

Phone: +5934435460663

Job: Central Hospitality Director

Hobby: Yoga, Electronics, Rafting, Lockpicking, Inline skating, Puzzles, scrapbook

Introduction: My name is Clemencia Bogisich Ret, I am a super, outstanding, graceful, friendly, vast, comfortable, agreeable person who loves writing and wants to share my knowledge and understanding with you.